Har zuwa yanzu an gagara samun gamsashshen bayanai game da inda makudan kudade da suka kai naira triliyan ashirin (N20,000,000,000,000) suka shiga a tsakanin wasu hukumomin gwamnatin tarayya duk da cewa an bi dukkanin matakan da suka dace wajen samun bayanan.
A cewar majiyar a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2016, kudaden nan sun kai naira 20,000,000,000,000, amma bayan kimanin watanni biyu, har yanzu babu gamsashshen bayani da hukumomin gwamnati suka mayar ma kungiyar.
- Advertisement -
“Sakamakon cikakken nazarin wasikar da kuka aiko mana ta hannun mashawarcinku akan harkar sharia J.O Obule, ofishin sakataren gwamnati na ganin hukumar tattara kudaden haraji na kasa, FIRS ce tafi dacewa ta amsa tambayoyinku.
#Mikiya