-Advertisement-


An Nada Alhaji Nastura Ashiru Sharif A Matsayin Uban Kungiyar Arewa Media Writers Na Kasa


0 290

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Kungiyar Arewa Media Writers

-Advertisement-

-Advertisement-

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani wato “Arewa Media Writers” ta kasa karkashin jagorancin shugaban Kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, ta nada shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa Alhaji Nastura Ashiru Sharif a matsayin uban kungiya na daya (PATRON I) a matakin kasa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 614

-Advertisement-

Kungiyar ta bashi matsayin ne bisa cancantar shi da kuma jajircewar sa na kokarin da yake wajan bawa yankinmu na Arewa gudummuwa a matsayin shi na shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa.

A yau kungiyar “Arewa Media Writers” tayi tattaki har zuwa gidan shi dake jihar Kano, tare da sauran shugabannin kungiyar na kasa, ta bashi shaidar zama Uban wannan Kungiya mai albarka na daya a matakin kasa.

A yayin bashi shaidar zama uban wannan kungiya Alhaji Nastura Ashiru Sharif ya godewa wannan kungiya bisa kokarin da suke kan abinda ya shafi Arewa sannan ya baiwa Kungiya shawar wari masu amfani domin gabatar da ayyuka kan tsari.

Haka zalika Kungiyar tayi kira ga Al’umma da su bawa kungiyar hadin kai tare da goyon baya domin kawo wa yankin Arewa da Nigeria baki daya cigaba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.