An Kashe Wani Karamin Yaro Ta Hanyar Rataya A Kano


0 308

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Wasu da ba a san ko su wanene ba sun shiga har gida sun rataye Najeeb Kamal A Baba an kashe shi har lahira. Bayan an tashe su daga Makaranta, mahaifinsu ya ɗauko su, da shi da ‘yan uwansa (Nauwar da Nabeel), ya kawo su Gida.

Lamarin ya auku ne a bayan Gidan Maitangaran dakw unguwar Gadon Kaya a Kano.

Da yammacin jiya Alhamis da misalin ƙarfe 5:00 aka kira mahaifinsa yana kasuwa wurin nema, sai mai ɗakinsa ta kirashi waya tana kuka, tana cewa Najeeb yana suma, sai ya taso da sauri ya nufo gida, yana zuwa asibiti likitoci suka duba sai suka ce mashi ya yi hakuri Allah ya karɓi abin sa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Bayan ya dawo gida da dare sai ya ga igiya a ɗaure a jikin ƙofa a cikin gidansa, wanda hakan ya tabbatar mashi cewa lallai rataye Najeeb aka yi, akwai ɗansa Nabeel (ƙani ne a wurin marigayi Najeeb ɗin) ya ce yaga lokacin da almajirinsa ya cire marigayin daga jikin igiyar da aka rataye shi ya kwantar da shi a ƙasa.

Jami’an tsaro da Likitoci sun gama binkicen su sun bada gawar sa, a cewar mahaifin marigayin da aka kashe Alh Kamal A. Baba

Tuni dai aka yi jana’izar yaron a bayan sallar Juma’a.

Allah kajikansa. Allah katona asirin wanda suka aikata hakan.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.