Labarai

An Kashe Shugaban ISWAP, Albarnawi A Borno

Daga Sulaiman Ibrahim,
An kashe jagoran kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP), Abu Musab Al-Barnawi a jihar Borno, kamar yadda jaridar Daily trust ta bayyana.

An ba da rahoton cewa an kashe shi a makon da ya gabata na watan Agusta, na wannan shekarar.

Al-Barnawi shi ne dan wanda ya kafa Boko Haram, Mohammed Yusuf wanda shi ma jami’an tsaro suka kashe shi a shekarar 2009 lokacin da ya kaddamar da yaki da gwamnatin Nijeriya.

Fiye da mutane dubu daya ne suka mutu a lokacin tada kayar bayan.

A shekarar 2016, kungiyar IS mai da’awar kafa daular Musulunci ta sanar da Al-Barnawi a matsayin shugaban kungiyar da ke da alaka da Boko Haram ta Yammacin Afirka, wacce Abubakar Shekau ya jagoranta.

Yadda aka kashe Al-Barnawi

Wata majiya tace, rundunar sojin Nijeriya ce ta Kashe shi, sabanin wacce tace ya mutu ne yayin fafatawa a tsakanin sansanin su na ISWAP.

Hausa leadership

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: