Labarai

An kashe DPO yayin rikici da ‘yan Okada a Legas

An kashe wani mukaddashin sifritandan dan sanda na Najeriya wato DPO mai suna Kazeem S Abonde yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da ‘yan Okada a yankin Ajao da ke jihar Legas.

Rahoanni sun ce lamarin ya auku ne yayin da ya jagoranci wata tawagar jami’ansa don tarwatsa matukar babura masu kafa biyun da aka fi sa da ‘yan Okada da ke tare hanya.

Jaridar Daily Post Nigeria ta ce yayin hargitsin ne jami’ansa suka watse don buya, lamarin da ya sa abokan fadan nasu suka cim ma sa.

An kone motocin ‘yan sanda biyu a yayin rikicin.

Kafin rasuwarsa shine DPO din Ajangbadi.

Sulaiman Lawan

Sulaiman Lawan Usman is a graduate in Bsc Mechanical engineering from Kano University of Science and Technology, Wudil. Also a founding member of ArewaBlog. And now he is working with Vision FM Nigeria as Head of engineering

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: