An karrama Dabo Daprof Da Gwarzon M.C A Arewa A karo Na Biyu


0 334

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An gudanar da taron karramawar ne dake cike da kayatarwa ga mawakan jahar Kano, dama na wasu makwabtan jahohi wadan da suka sheda yadda bikin ya gudana cikin tsari mai daukan hankali.

Bikin karramawar wanda kungiyar Rhymes Pillars Crew ta shirya wanda ya hadar da bada lambar yabo, gudanar da gasa da kuma gabatar da wakewake daga mawaka.

Bikin wanda aka gabatar a ranar lahadi biyar ga watar mayu ta shekarar 2019 a tsakiyar birnin Kano, ya samu halattar mawaka daga masana’antar Hausa Hip Hop dana takwarar ta Kannywood.

An karrama mawaka da yan film a rukuni daban daban a gurin taron, inda Dabo Daprof wanda shi yayi M.C a wajan taron ya koma gida da lambar yabo na kwarzon M.C a Arewa.

Wannan shine karo na biyu a cikin shekara ta biyu kenan yana samun wannan lambar yabon a jere, kuma babu shekka ya chanchanci wannan lambar yabon duba da dadewa, kwarewa da kuma tasirin sa a wannan fanni na M.C. Dabo Daprof wanda mawaki ne mai dumbum basira a fanni daban daban, daya ne daga cikin manyan mawaka a Arewa wanda nasarar sa da kuma gudunmawar sa a cikin masana’antar Hausa Hip Hop take amo ga kunnuwar mutane da dama.

Ya sadaukar da lambar yabon ga abokan sa mutum biyu a wajan taron, wato (Stainless daya daga cikin manyan mawaka mata masu rapping a Arewa, da kuma Icon Faruoq daya daga cikin matasa masu tasiri a Arewa) wadan da ya kira su dan su karbi lambar yabon a madadin sa.

Ya kuma gode wa wasu mawakan da suka halacci bikin, sannan suma ya sadaukar da lambar yabon gare su.

Wasu daga cikin manyan mawakan da suka samu lambobin yabo a wajan taron sun hadar da TY Shaban, Gambo D. Guy, Sonikman, Hausatop, MSK, Mkay, AleeGee, Stainless, Madox, Genius, Dj Speysh, Tita Hot, Dj Waziri, Sai’d Gadan Kaya, Umar M. Lawan, Mamee da sauran su, wasu wadan da suka samu lambar yabo suma amma basu samu damar halattar taron ba sun hadar da Billy-O, Doctor Pure, Ado Gwanja, Bello Vocal, da dai sauran su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Bikin ya dauki hakali domin an yi shi ne a daran karshe kafin watar Ramadan na shekarar 2019.

Daya daga cikin manya kampanukan sadarwa a Africa wato kampanin M.T.N sun halacci wajan bikin domin bada kyaututtuka ga wadan da suka ci gasar dama wasu manyan mawakan da suka halacci taron.

Dabo Daprof wanda mawaki ne mai lambobin yabo da dama a fannoni daban daban kuma wanda ya fara harkar waka a matsayin rapper, sannan daga bisani ya fara singing kuma tun daga lokacin ya kara shura da daukaka sannan ya zamo jagaba a fannin salon wakar da aka fi sani da Hausa Afro pop.

Yayi performing din daya daga cikin wakokin sa da yake kan tashe yanzu a wajan bikin mai suna “Tawa ce” tare da daya daga cikin manyan mawaka da suka kware wajan wakar R and B wato Sonikman a karo na farko tun bayan sakin wakar.

Wakar wacce Sonikman din ne yayi producing kuma gidajan radio da dama suke saka ta a koda yaushe tun bayan fitowar wakar a karshen shekarar 2018 ta zamo tamkar hantsi neka gidan kowa.

Don samu karin bayane ko labarai a kan Dabo Daprof, sai ku cigaba da ziyartar shafin mu akai akai. Sannan zaku iya bin Dabo Daprof a shafikan sa na yanar gizo kamar haka :

Instagram:
@dabo_daprof
@dabodaprof

Twitter:
@dabo_daprof

Facebook:
Dabo Daprof

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.