Kannywood

An karrama Ali Nuhu da Adam Zango a London

Adam Zango ya zama cikakken jarumi
An karrama wasu daga cikin taurarin fina-finan Hausa da aka fi sani da ‘Kannywood’ a wani biki da aka gudanar da birnin London.
A bikin ‘African Film Awards’, fitaccen tauraron Kannywood, Ali Nuhu da Adam A Zango da kuma Hafizu Bello duk sun samu kyautuka.
Ali Nuhu wanda ke fitowa har ma a fina-finan Nollywood ya samu kyautar bajinta ta wanda aka dade ana damawa da shi.
A yayin da Adam A Zango, wanda shi ne tauraron fim din ‘Gwasko’ da aka fitar a bana, ya samu kyautar fitaccen tauraron fim.
Shi kuma Hafizu Yahaya an ba shi kyautar mai bada umurnin da ya fi kowanne a bana a fina-finan Kannywood.
An shafe shekaru 19, ana gudanar da bikin ba da kyauta ga jaruman fina-finan Najeriya na ‘African Films Awards’ a London, amma sai a bana aka bai wa jaruman fina-finai na Kannywood.
Ali Nuhu na ci gaba da haskakawa
‘Yan Najeriya mazauna London da kuma dalibai sun halarci bikin da aka gudanar a yankin gabashin London domin ta ya jaruman murnar samun kyautukan.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement