Labarai

An Kammala Aikin Gina Gidaje Hamsin Da Gwamna Mai Mala Ya Gina A Garin Nangere

An kammala aikin gina gidaje 50 da Gwamna Mai Mala Buni ya gina a garin Sabon Garin Nangere a karamar hukumar Nangere.

Gina rukunin gidaje a fadin jihar Yobe na daga cikin manyan ayyuka da Gwamna Mai Mala Buni yake yi domin samar da muhalli ga masu karamin karfi. Samar da gidaje yana daga cikin hanyoyin rage talauci da kuma inganta zamantakewa da rayuwar iyali. Gwamna Mai Mala Buni yana da shirin gina gidaje 3,600 a duk kananan hukumomin jihar Yobe domin tallafawa wajen shawo kan matsalar muhalli.

Daga Isa Sanusi
Babban mai taimakawa
Gwamna Mai Mala kan harkokin
Yada labarai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: