An Kama Wasu Mutane Hudu Dake Yi Wa `Yan Ta`adda Safarar Man Fetur A Jihar Katsina


0 346

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar kama wasu mutane hudu da ake zargin su da yi wa ‘yan ta’adda safarar man fetur a jihar Katsina.

Wannan na kunshe ne a takardar da kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambi Isa ya sanyawa hannu aka raba ta ga manema labarai.

‘Yan sandan sun yi nasarar kama wadanda ake zargin ne a yayin da suka fita farauta a kananan hukumomin Batsari da Dutsimma.

Wadanda aka kama sune;

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Zaharadeen Mas’udu, daga Unguwar Alkali Quarters, Katsina

Ibrahim Khalid, mai shekaru 28 daga Sabon Gida Quarters, Katsina

Najib Dayyabu, mai shekaru 17 daga Unguwar Sarki, karamar hukumar Batsari a Katsina

Halliru Yarima mai shekaru 30 daga Unguwar Yarima Quarters, a karamar hukumar Dutsinma, Katsina

Abubuwan da aka kama su da shi sune jarkokon man fetur guda 33 da jarkoki 24 da babu komai a ciki.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.