Labarai

An Kama Wani Inspektan Dan Sanda Da Buhuhuna 75 Na Tabar Wiwi

Hukumar hana safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA reshen jahar Kogi ta kama wani inspektan dan sanda, da wani korarran soja da kuma wasu mutane guda 12 dauke da tabar wiwi kimanin kilo 1,083.62 wanda farashin su ya kai naira miliyan 6.
Kwamandan hukumar Idris Bello ya bayyana wa manema labarai a yau Litinin cewa an kama Inspektan dan sandan ne a ranar 25 ga watan Fabrilu a yankin Crusher da ke Lokoja, babban birnin jahar Kogi.
Ya ce an kama shi ne dauke da buhuhuna 75 na wiwi wanda ya sanya a cikin wata motar ‘yan sanda mai lamba NPF 7973 NPF.
Ya kara da cewa, inspektan na kan hanyar sa na kai tabar mai nauyin kilo 818.2 jahar Edo ne a lokacin da ya shiga hannu, tare da wadanda suka hada baki guda 2.
Sai kuma korarran sojan wanda shi kuma aka kama shi akan hanyar sa ta zuwa Lokoja daga jahar ta Edo dauke da kilo 44 na tabar wiwi.
Banda wadannan mutanen, jami’an hukumar sun kuma kama mutane 12, a ciki har da mace guda daya dauke da adadi daban daban na tabar.
Bello ya alakanta nasarar da hukumar ke samu a kwanakin nan da taimakon da gwamnatin jahar a karkashin shugabancin gwamna Yahaya Bello ke basu, ya kuma godewa gwamnan game da motocin sintiri da ya kara masu.