An Kama Maza Karuwai Masu Damfara a Kano

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Sufurtanda Magaji Musa Majiya ya ce matasan sun yi ta bibiyar wani attajiri har suka kulla alaka da shi, sannan suka fara yi masa barazana

Rundunar `yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta cafke wasu mutum biyu da take zargin ‘yan luwadi ne, wadanda ke amfani da kafofin sada zumunta na zamani suna tallata kansu.

Binciken da rundunar ta yi ya nuna cewa mutanen su kan fara ne da kulla zumunci da mutane, amma daga baya sai su nemi a yi lalata da su, har su kan yi barazanar bata wa mutum suna idan bai ba su hadin kai ba.

Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Sufurtanda Magaji Musa Majiya ya ce matasan sun yi ta bibiyar wani attajiri har suka kulla alaka da shi, sannan suka fara yi masa barazana.

“Daga farko sun fara kiranshi ne suna yi masa godiya a matsayin makoci ne ko mai hali da yake taimakawa… Daga karshe kuma sai suka bi shi da cewar ya ba su kudi. Ya ce kudin me? Sai suka ce kudin da ya yi amfani da shi,” in ji Majiya.

Wannan layi ne
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

‘Yan sandan sun ce mutanen sun yi wa mutumin barazana cewa idan bai ba su kudi ba to za su bata masa suna a shafukan sada zumunta cewa ya yi lalata da su.

Babban Sufurtandan `yan sanda Magaji Musa Majia, shi ne Kakakin rundunar, kuma ya kuma shaida wa Ibrahim Isa cewa daga haka ne aka tsaurara bincike aka kuma kama su.

“Daya daga cikinsu ma ya tabbatar mana da cewa tun yana yaro wani dan uwansa ya fara lalata shi har shi kuma ya wuce da haka,” in ji Sufurtanda Majiya.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar:

Luwadi ko madigo haramtaccen abu ne a tsarin dokokin Najeriya.

handcuffHakkin mallakar hoto
Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: