Labarai

An kama mata 2, ɗaya ta yi garkuwa da ƴarta, ɗayar kuma da ɗan ɗan’uwanta a Kano 

An kama mata 2, ɗaya ta yi garkuwa da ƴarta, ɗayar kuma da ɗan ɗan’uwanta a Kano

Ƴansanda sun kama wasu mata biyu, Rahma Sulaiman, yar shekara 25 da kuma Zainab Rabi’u ƴar shekara 45 a jihar Kano.

 

Tushe: Daily Nigerian Hausa.

Ƴansandan sun ce Rahma ta yi garkuwa da ƴarta ta cikinta, inda ita kuma Zainab ta sace ɗan dan’uwanta.

A yayin da Rahma ta yi garkuwa da ‘yarta ‘yar shekara 6, Hafsat Kabiru tare da neman kudin fansa naira miliyan uku daga wajen tsohon mijinta, Kabiru Shehu; Zainab kuma, a ɗaya ɓangaren, ta yi garkuwa da dan uwanta kuma ta bukaci a biya ta Naira miliyan 20 daga hannun yayan na ta.

Kwamishinan ƴansanda na jihar, Mohammed Gumel, ya tabbatar da kamen a lokacin da yake gabatar da matan tare da wasu mutane 13 da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma dillalin miyagun kwayoyi a shelkwatar rundunar da ke Bompai a jiya Alhamis.

Gumel ya ce, “A ranar 08/05/2023, an samu rahoto daga wani Kabiru Shehu da ke Sharada Quarters, Karamar Hukumar Kano Municipal, cewa matarsa ​​da ya saki, Rahma Sulaiman, ‘yar shekara 25, ta shaida masa cewa an sace ‘yarsa ‘yar shekara 6 da haihuwa, mai suna Hafsat Kabiru, kuma wasu da ba a san ko su waye ba sun kira ta ta wayar salula su na neman kudin fansa naira miliyan uku (N3,000,000:00k).

“A binciken da aka yi, an ceto yarinyar a karamar hukumar Madobi. An kama matar ta kuma amsa cewa shirya garkuwar ta yi, inda ta kai diyar ta ta wani maboya, sannan ta bukaci a biya ta kudin fansa.

“Wani lokaci a ranar 04/04/2023, mun samu rahoto daga wani mazaunin Kofar Ruwa Quarters, cikin karamar hukumar Dala, Jihar Kano, cewa an yi garkuwa da dansa, Almustapha Bashir, mai shekaru 6, kuma sai an biya kudin fansa Naira Miliyan Ashirin (N20,000,000). :00). Daga baya aka yi ciniki aka daidaita a kan Miliyan Biyar da Dubu Dari da Hamsin (N5,150,000:00).

“A ci gaba da bincike, an ceto yaron ba tare da jin rauni ba, sannan an kama wacce ake zargin, Zainab Rabi’u, ‘yar shekara 45 a unguwar Gwammaja, wacce ita ce ta shirya garkuwar.

Sauran sun hada da Abdurrashid Sa’idu mai shekaru 27 da Hassan Abdullahi mai shekaru 24 da Ahmed Saleh mai shekaru 25 duk a Sheka Quarters Kano. Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike,” in ji Mista Gumel.