Labarai

An kama ƴan ta’adda 5 a Kaduna da Kano 

An kama ƴan ta’adda 5 a Kaduna da Kano

Jami’an tsaro na farin kaya, SSS, Sojoji da yansanda sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin cewa yan ta’adda ne a wani samame da a ka kai kan maboyar ‘yan ta’adda a sassan jihohin Kaduna da Kano.

Dokta Peter Afunanya, jami’in hulda da jama’a na hukumar ta SSS ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a Abuja.

Ya ce an kai farmakin ne a maboyar yan ta’adda jihohin biyu a lokaci guda da sanyin safiyar jiya Litinin.

A cewarsa, a lokacin da aka kai samame a jihar Kaduna, ‘yan ta’addan sun ta tada bama-bamai a kan dakarun da ke yaki da su.

Ya ce daya daga cikin ‘yan ta’addan da ke sanye da rigar kunar bakin wake ya tarwatsa kansa yayin da aka kama mutane uku da ake zargi.

 Afunanya ya ce kayayyakin da aka gano a yayin bincike a gidan kungiyar, bayan da ‘yan sandan kunce bam , EOD suka kunce wasu bama-bamai, akwai jaket din kunar bakin wake guda biyu, bindiga AK-47 daya, bindiga da kuma kwamfutar tafi-da-gidanka daya.

A jihar Kano, an kama wasu mutane biyu da aka kwato, bindigu, wayoyin hannu 11, gurnetin hannu guda biyu, da kuma gidan jera harsashi AK-47 cikakke.

Afunanya ya ce tun da farko bayanan sirri sun nuna cewa manyan ‘yan ta’adda na taruwa a yankin Arewa maso Yamma domin aiwatar da munanan ayyuka a yankin.

 

Daily Nigerian Hauss.