-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

An Kai Buhari Kotu Kan Kin Bincikar Ganduje


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wata kungiyar da ke fafutukar ganin an yaki cin hanci da rashawa da kuma kokarin tabbatar da adalci SERAP, ta shigar da karar Shugaba Muhammadu Buhari, kan abun da ta kira “kasa bai wa ministan shari’a umarnin bincikar badakalar cin hanci da ake zargin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da shi.

Kungiyar ta shigar da karar ne a wata babbar kotu da ke Ikoyi a jihar Legas.

A watan Nuwamba ne dai kungiyar SERAP ta umarci shugaban kasar da ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan Gwamna Ganduje, tana mai cewa “domin gurfanar da shi a gaban kotu a karshen wa’adinsa idan an samu kwararan hujjoji.”

Haka kuma kungiyar ta bukaci a bai wa dan Ja’afar Ja’afar kariya, wato dan jaridar da ya wallafa bidiyon da ke nuna gwamnan yana karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila a jihar

SERAP ta ce har yanzu Shugaba Buhari bai ce komai ba tun bayan da ta gabatar masa da wasikar neman ya yi wannan abu.

A makon da ya gabata, wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da majalisar jihar daga ci gaba da binciken da ta fara na zargin karbar cin hancin dala miliyan biyar din da ake yi wa Gwamna Ganduje.

Wannan layi ne

Waiwaye

A watan Oktoba ne aka fara yada wasu bidiyoyi da ake zargin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hanci daga wajen ‘yan kwangila.

Daga bisani majalisar dokokin jihar ta gayyaci editan kafar yada labarai ta Daily Nigerian Jafar Jafar game da bidiyon da ya wallafa din.

Jafar
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

An gayyaci mawallafin jaridar ne don ya ba da ba’asi a gaban kwamitin da majalisar ta kafa don binciken bidiyon.

Sai dai gwamnatin ta Kano ta kai karar jaridar da ta fara wallafa bidiyoyin da mawallafin jaridar kara kotu bisa zargin bata suna.

Haka kuma wata kotu ta dakatar da majalisar Kano daga ci gaba da gudanar da bincike kan zargin karbar cin hancin.

Mene ne a cikin bidiyon?

A ranar Lahadi ne Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian ya saki wannan bidiyo, wanda ake zargin wani dan kwangila yana mika wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bandir-bandir na dalolin Amurka.

Jim kadan da fitar bidiyon, gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwa tana karyata lamarin, tare da yin barazanar kai karar Jaafar Jaafar kan abun da ta kira bata sunan gwamnan.

Mawallafin bidiyon ya ce zai ci gaba da fitar da bidiyon.

A cikin bidiyon dai da a ka saki na farko babu murya sai kidan sarewa, al’amarin da wasu ke ganin shirya shi kawai aka yi.

Sai dai a bidiyo na biyu da ya saki ranar Litinin, an jiyo muryar wanda ake zargin dan kwangilar ne yana umartar gwamnan da ya tashi tsaye yana cewa “ban sani ba ko tashi za ka yi a dinga mika ma, a aljihunka sai sun fi zama lafiya”.

Wannan al’amari dai na ci gaba da janyo ce-ce ku-ce a Najeriya musamman a kafofin sada zumunta.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: