Labarai

An Haramta Bikin Murnar Sanya Hannu A Riguna A Yayin Murnar Kammala Karatu Ga Ɗaliban

An Haramta Bikin Murnar Sanya Hannu A Riguna A Yayin Murnar Kammala Karatu Ga Ɗaliban Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Adua, Da Ke Katsina

Daga Zaharaddeen Gandu

Shugabannin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina (UMYUK) sun sanar da hana sanya hannu kan ƙananun riguna masu nuna tsiraici ga ɗaliban da suka kammala karatunsu a jami’ar, duba da irin yadda ɗaliban ke nuna rashin kunya da baɗala a yayin murnar kammala karatu da sunan sanya-hannu (Sign Out).

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata madauwari daga ofishin shugaban kula da harkokin ɗalibai na ranar 24 ga Yuni, 2021 kuma sa hannun Dean, Mustapha Bala Rumah.

Sanarwar ta karanta sashi kamar yadda ta bayyana “Gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta lura da damuwa, yadda ɗaliban da suka kammala karatu suke bikin murnar ficewarsu bayan jarabawar ƙarshe da suka yi musamman sanya hannu kan ƙaramar riga mai fidda tsiraicin sassan jikin mace, yayin kammala karatun”.

“Sakamakon haka ne, Hukumar Jami’ar ta hana sanya hannu a kan rigunan ga bikin kammala karatun. Da fatan za a sanar da ku cewa, za a ɗauki babban matakin da ya dace a kan waɗanda suka saɓawa dokar.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: