An haifi jaririya mai kai biyu a Sokoto

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

An haifi jaririyar mai kai biyu a asibitin General Hospital wanda ke karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sakkwato.

Mahifiyar jinjirar ta isa asibitin ne da misalin karfe biyar a ranar Alhamis din da ta gabata bayan da ta shafe sa’o’i tana nakuda a gida, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wata jami’an asibitin ta gano cewa matar ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda jinjirar ta zo da kaffafu maimakon da kai, sai ta bukaci taimakon likitoci a asibitin.

LLikitocin ne suka gudanar da bincike kan matar kuma suka gano cewa jaririyar ta riga ta mutu saboda dadewar da matar ta yi tana nakuda kafin ta je asibitin.

Daya daga cikin likitocin da suka duba matar, Dokta Malami Muhammad Gada ya ce sun fuskanci matsaloli da dama wajen kokarin fida jinjirar saboda yadda kan ta yake da nauyi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 27

”Matar ba ta taba zuwa awon ciki ba lokacinda take da juna biyun, lamarin da ya janyo ba a iya gane yanayin jinjirar ba da wuri,” in ji shi.

Likitocin sun kadu sosai bayan da suka fida jinjirar saboda irin halirtar da aka haife ta da ita.

Ya bayyana cewa dadewar da matar ta yi kafin ta haihu shi ne ya janyo mutuwar jaririyar.

A cewar likitar, abin da ke janyo a haifi jariri cikin irin wanan yanayin ita ce wata matsala da kan iya samun masu ciki wacce a Turance ake kira ”Congenital Anomalies”.

Masana da dama suna ganin cewa shan wasu magungunan da ba su kamata ba a yayin da mace take dauke da juna biyu suna iya shafar halirtar jariri.

”Ana samun jariran da ke fama da irin wanan matsalar da dama kuma su kan rayu,” a cewar Dokta Gada.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.