Labarai

An Gano Wata Kungiyar NGO Tana Koyawa Wasu Mutane Harbi A Wani Otel A Jihar Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bada umurnin a dakatar da wata kungiya mai zaman kanta (iNGO) biyo bayan samun kungiyar da koyar da harbi a wani Otel a jihar Borno.

Mai magana da yawun gwamnan Borno, Isa Gusau, shine ya sanar da umurnin gwamna Zulum na dakatar da kungiyar, inda yace an sami kungiyar mai suna (iNGO) wacce ta fito daga kasar Faransa tana koyar da harbi da bindigar roba a wani Otel dake titin Circular a Maiduguri.

Gusau, ya kara da bayyana cewa makwaftan Otel din ne suka ji karar harbe-harben bindiga a cikin Otel din kafin daga bisani mahukuntan gwamnati suka kai rahoton ga ofishin ‘yan sanda dake kula da yankin da Otel din yake a GRA.

Bayan gabatar da bincike ‘yan sanda sun kama bindigogin roba huda 3 a Otel din da wasu mutum 2 masu horar da harbin yanzu haka suna hannun ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Daga Dahiru Mukhtar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: