Get New DJ Mixes
Labarai

An Fara Sanyawa Shanu Na’urar Da Zai Kawo Karshen Fashin Su

A wani yunkuri na kawo karshen fashin shanu a Nijeriya, an fara sanyawa masu wata na’urar da za a iya gano duk inda suke.
Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa da Dr. Aliyu Tilde ya yi a shafinsa na Facebook, inda ya ce da zaran an kama shanu mai dauke da wannan na’ura za’ a san daga inda suka fito.
A cewarsa,“Karshen satar shanu ya zo, dazun nan Malaman shanu suka bar gidana bayan sun saka wa kowacce saniyata wani digon na’ura a cikin jiki wanda zai taimaka wajen gano duk inda take a duniya. Wannan ba karamin ci gaba ba ne”.
Ya bayyana farashin na’urar a mastayin N2,000 kacal.
Ya ce Idan barayin shanu suka gane cewa ba za a iya sayen shanu ba, ko a yanka ta, ko a loda ta a mota ba tare da an san mai ita ba, dole ne su nemi wata sana’ar daban.
Daga karshe ya yi kira da a sanar da makiyaya da manoma wannan gagarumin ci gaba da aka samu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.