Kannywood

An dinke baraka tsakanin ‘yan fim a Kano

Sama'ila Afakalla shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano
Hukumomi a jihar Kano na kokarin ganin an tsaftace harkar fina-finan Hausan.

An dinke barakar da ke tsakanin ‘yan fim a jihar Kano ta hanyar kafa wata sabuwar kungiya.

A hirar da BBC ta yi da Sa’idu Gwanja tsohon shugaban kungiyar ‘yan fim a Kano, ya ce sabuwar kungiyar gamayyar kungiyoyin shirya finai-finai ce wacce ta kunshi daidaikun kungiyoyin shirya fina-finai na ‘yan wasa da marubuta da masu ba da umarni da kuma sauran masu ruwa da tsaki a Kanywood.
Manyan jami’an gwamnatin jihar Kano ne su ka halarci kaddamarwar, ciki har da kwamishinan yada labarai da mai ba gwamna shawara a harkar addinai da kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar.

A cewar tsohon shugaban masu shirya fina-finan, ana tafka asara a kasuwa a sanadiyyar yawan fina-finan da ake fitarwa a kowanne mako wanda aka danganta ga rashin hadin kai a tsakanin masu sana’ar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.