Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da bukukuwan Babbar Sallah da hawan Sallah ga masarautu Biyar din dake fadin jihar saboda annobar cutar Korona.
Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana haka a wani taron ‘yan jaridu daya gudana a ofishinsa.
- Advertisement -
Muhammad Garba ya ce duka masarautu biyar din dake fadin jihar zasu gabatar da sallar idinsu a masarautun su domin bin tsarin kariya daga cutar Korona
Tun lokacin da aka saka Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero dai har yanzu baiyi hawan Sallah ba sakamakon cutar Korona.