Daga Muhammad Adamu Yayari
Mai martaba sarkin Deba Alh. Usman Ahmad Muhammad II, ya dakatar da wasu hakimansa guda biyu na Gundumar Garin Malam da Wajari bayan da suka shirya addu’a ta musamman ga shugaban kasa buhari.
- Advertisement -
Takardar ta katarwa wacce take dauke da sa hanun sakataren masarautar Alh. Sa’idu Mele ta bayyana cewar “mai martaba Sarkin Deba ya dakatarku saboda wasu munanan dalilai, Adon haka ana fatan zaku daina yin kowa ne irin ayyuka da sunan masu sarautun gargajiya” kamar yadda yake a takardar.
A zantawar da Hakimin Garin Malam Alh. Julde yayi da jaridar Premium Times ya bayyana cewa da gaske an dakatar dasu saboda suna shirya zikiri da addu’o’i wa shugaban kasa.
Alh. Julde ya kara da cewar ya tabbatar da cewa Sarkin Deba Umarnin da katar dasu aka bashi Daga Gwamnatin jihar Gombe.