An Dage Hawan Sallah A Katsina


0 136

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fadar masarautar Katsina ta fitar da wata sanarwar, wadda a ciki ta aike sakon jaje ga daukacin jama’arta kan ibtila’in kashe-kashen da mutanen gundumomin Batsari, da Dan-Musa, da Kankara da Wagini da sauransu wuraren da abun ya shafa suka samu kansu a ciki.
Sakataren masarautar Alhaji Bello M IFO shi ne ya fitar da ita, tare da shaida wa jama’a ce wa sakamakon halin da suka samu kansu a ciki na alhini da jimami, masarautar ta yanke shawarar a wannan karon ba za a yi hawan sallah kamar yadda aka saba ba.
Alhaji Bello ya ce Mai-martaba sarkin Katsina Dr Alhaji Abdulmumin Kabir Usman CFR, da majalisar masarautar ne suka ga dacewar dage duk wasu shagulgula don nuna alhini kan abin da ya samu jama’arsu.
A karshen sanarwar ta ce za a je sallar idi kamar yadda aka saba, da yin addu’o’in neman zaman lafiya ga jihar Katsina da Najeriya baki daya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.