An gudanar da taro a tsakanin Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad, wacce Sakataren Ma’aikatar Kudi ya wakilta da Babban Bankin Nijeriya da Ofishin dake kula da basuka da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka cimma matsaya da Kungiyoyin dillalan man fetir na kasa akan cewa za a ci gaba da lodi da kuma sayar da albarkatun man fetir ba tare da wata matsala ba.
Hadakar kungiyoyin dillalan man fetir din har ila yau, sun ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa ba za a samu wahalar manfetir ba a yayin da ake tunkarar bukukuwan karshen shekara.
Duk da haka, za a ci gaba da tattaunawa a tsakanin gwamnatin tarayya da Kungiyoyin dillalan manfetir din don samun maslaha ta din-din-din akan al’amarin.
#RARIYA