Labarai

An ceto wata daga cikin ƴan matan Chibok Bayan shekaru 9 a hannun Boko Haram

An ceto wata daga cikin ƴan matan Chibok Bayan shekaru 9 a hannun Boko Haram

Kwamandan ‘Operation Hadin Kai (OPHK)’, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya ce an kubutar da wata ƴar makarantar Chibok.

Sojojin kasa ne su ka ceto Saratu Dauda mai shekaru 25 a ranar 6 ga Mayu, 2023 a maboyar ƴan ta’adda mai suna Ukuba a dajin Sambisa, jihar Borno.

 Da take miƙa Saratu ga Kamar Ali, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Cigaban Jama’a, Hajiya Zuwaira Gambo, a yau Litinin a Maiduguri, ta bayyana cewa: “Kafin a cece ta bayan ta tsere, Saratu ta auri Abu Yusuf, wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram. “.

Janar Ali ya bayyana cewa, Saratu ta bar ‘ya’yanta uku tare da mijin nata da aka tilasta mata aurensa, inda su ka nemo hanyar fita daga dajin Sambisa, ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin ceto sauran yaran da ke hannun mijin Abu Yusuf.

Ya ce an garzaya da ita asibitin sojoji na Maimalari domin samun kulawa ta musamman; kafin mika ta ga gwamnatin jihar.

Kalaman sa: “Mun gode wa Allah da ya kubutar da Saratu Dauda. Wannan zai ba ku damar samun ingantacciyar rayuwa tare da iyayenku da sauran iyalai a garin Chibok.”