Labarai

An Buɗe Katafaren Garejin Gyaran Motoci Na Mata Zalla Karon Farko A Jihar Sokoto

Daga Comr Nura Siniya

Shugaban hukumar fasahar zana sanfurin motoci da tsarasu ta Najeriya (NADDC) Engr, Jelani Aliyu, ya kaddamar da garejin gyaran motoci na mata zalla domim bunkasa cigaban harkokin mata ta hanyar yaki da zaman kashe buje a jahar Sokoto.

Dukkanin matan sun samu horo na musanman, inda suka samu kwarewa ta fuskar magance ciwukan kowace irin mota.

Gidauniyar bunkasa cigaban mata ta (Nana Foundation) ce ta samar da garejin gyaran motocin da nufin nunawa duniya irin ƙoƙarin da mata za su iya yi a harkokin rayuwa daban daban.

Tabbas mata abin alfahri ne, domin suna bada gudunmuwa ga dukkan bangarori na cigaban rayuwa.

Allah Ya sanya albarka a cikin sana’oin mu na yau da kullum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: