Labarai

An bar jihar Katsina baya wajen rijistar zaben da INEC ke gabatarwa yanzun haka a intanet

Ka karanta yadda za ka shiga ka yi taka rijistar cikin sauki a wayarka ta hannu

Daga, Ibrahim M Bawa

Da farko za ka fara shiga wannan adireshin da hukumar zabe ta kasa INEC ta fitar don masu yin rijistar farko ko sabunta tasu sai su latsa

https://cvr.inecnigeria.org/

Bayan haka, zai bude maka, sannan sai ka shiga inda aka rubuta rijista, a nan za ta nuna maka abubuwa da yawa, kamar sabuwar rijista ce za ka yi? Ko sabuntawa ko gyara da makamantan irin wadannan.

A nan abin da za ka shi ga, kai mai son yin sabuwar rijista, sai ka ahiga new registration.

Kana dannawa za ta nemi ka fara sa Google account (Gmail) dinka, inda ta karba, za ka ci gaba da sa bayananka, sunan yanka, adireshi, hoto da sauransu, har ka zo inda za ka sa submit, in komai ya yi daidai, za ta nuna maka an karbi bayananka cikin nasara.

Yan uwa a daje a yi sannan a tura labarin ko’ina domin wanda bai yi ba ya samu ya yi, a rahoton INEC gaba daya yan Katsina mutum 983 ne suka yi rijistar har zuwa yammacin jiya Litinin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: