A Nigeria, matsalar satar shanu matsala ce da ta daɗe tana ciwa al’umma da hukumomi tuwo a ƙwarya.
Duk da cewa Nigeria na cikin ƙungiyar ƙasashe masu tabbatar da lafiyar dabbobi na duniya, rashin samar da hanyoyin tantance dabbobi a shekarun baya ya kasance wani babban ƙalubale ga ƙasar.
Wannan yasa wasu ƙwararru suka ɓullo da wata dubara ta amfani da fasahar zamani don tantance tare da gane dabbobin da aka sace.
An ƙaddamar da tsarin ne a Kaduna bayan nazari da masana kimiyya da likitocin dabbobi da masana harkar tsaro tare kuma da ƙwararru a harkar sadarwa suka yi na tsawon shekaru.
A cewar daya daga cikin jagorar shirin Malam Ibrahim Maigari Ahmadu, za’a riƙa sanyawa dabba wata ƙaramar na’ura kamar girma ƙwayar shinkafa mai lambobi a cikinta da za’a yi amfani da allura wajen sanya wa a cikin jikin dabba.
Ya ƙara da cewa duk dabbar da aka sanyawa na’urar za a iya gano ta a duk lokacin da aka sace ta.
Kungiyoyin Fulani a Nigeria dai sun bayyana gamsuwar su da ɓullo da wannan fasaha inda suka ce za ta taimaka wajen magance satar shanu a kasar.
Add Comment