Labarai

An Ɓarke Da Zanga-Zangar Rashin Nuna Goyan Bayan Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Ƙasa

DA ƊUMI-ƊUMINSA: An Ɓarke Da Zanga-Zangar Rashin Nuna Goyan Bayan Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Ƙasa

 

Daga Comr Nura Siniya

 

Wasu matasa masu rajin kawo sauyi a Najeriya mazauna babban birnin tarayya Abuja sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin goyon bayan rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar 29th May 2023.

 

Masu zanga zangar sun yi dafifi a harabar kotun Tirayabunal da ke Abuja ɗauke da alluna masu rubutu daban-daban inda suke ikirarin cewa rantsar da Tinubu a ranar 29, ga watan May 2023 babban yi ma dimokaraɗiyya zagon ƙasa ne da kuma cin amanar ƙasa.

 

Haka zalika masu zanga zangar sun yi ga hukumar zabe ta ƙasa INEC da ta gaggauta soke nasarar Tinubu kafin zuwa ranar rantsuwa.