-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Amurka Ta Taya Buhari Murnar Lashe zaben 2019


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin Amurka ta taya Shugaba Muhammadu Buhari murnan sake lashe zaben 2019.

A wata sanarwa mai dauke sa hannun Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ta yaba wa ‘yan Najeriya kan yadda suka fito suka kada kuri’unsu.”

“Muna sane da rahoton masu sanya ido na kasashen waje wadanda suka bayyana cewa zaben an yi shi cikin ‘yanci da adalci duk da cewa an dan samu tashe-tashen hankula nan da can.”

“Muna taya sauran ‘yan takarar da su ma suka fafata a zaben murna musamman yadda aka yi zaben cikin lumana.”

Haka kuma, sanarwar ta bukaci ‘yan kasar da su “tabbata sun yi sauran zabuka a mako mai zuwa cikin nasara,” in ji Mista Pompeo.

Karshen Facebook wallafa daga U.S. Embassy Nigeria

Amurka ta ce a shirye take wajen gannin ta yi aiki da Najeriya don samar da zaman lafiya da ci gaba tsakanin kasashen biyu.

A ranar Larabe ne aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.

Ita ma kasar Faransa ta bi sahun Amurkan, inda ta taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben a ranar Alhamis.

Hakazalika Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz shi ma ya aike wa shugaban da irin wannan sako.

Shugaban mai shekara 76, na jam’iyyar APC, ya kayar da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri’u kusan miliyan hudu.

Sai dai Atiku ya yi watsi da sakamakon zaben kuma ya ce zai kalubalance shi a kotu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

- Advertisement -

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: