Amurka Ta Bayyana Damuwa Kan Dakatarwa Da Sauya Alkalin Alkalai

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Amurka ta bayyana damuwa kan matakin bangaren zartarwar Najeriya na dakatarwa da kuma sauya Alkalin Alkalan kasar.

Sanarwar da ofishin jekadancin kasar a Najeriya ya fitar ta ce, Amurka ta damu sosai kan tasirin matakin da bangaren zartarwa ya dauka na dakatarwa da kuma sauya Alkalin Alkalai ba tare da goyon bayan majalisa ba yayin da babban zabe ke karatowa.

Talla

Sanarwar ta ce yadda matakin ya janyo suka game da cewa ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma ‘yancin bangaren shari’a, hakan na iya kawo cikas ga alkawalin da gwamnati da ‘yan takara da jam’iyyun siyasa suka yi na tabbatar da ganin an yi sahihi kuma karbabben zabe cikin kwanciyar hankali.

A ranar Juma’a ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalan kasar Walter Onnoghen tare da nada Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin na riko har sai an kammala shari’ar Onnoghen da ake tuhuma da kin bayyana dukiyar da ya mallaka kafin rantsar da shi a 2017.

Shugaban ya bayyana cewa kotun da’ar ma’aikata ce ta bayar da umarni a dakatar da shi har sai an kammala gudanar da shari’arsa.

Matakin dai ya janyo suka musamman daga bangaren ‘yan adawa da masana shari’a a Najeriya, inda wasu suka ce ya saba wa kundin tsarin mulki.

Amurka ta bukaci a kawo karshen wannan dambarwar ta hanyar bin matakan da suka dace kuma cikin kwanciyar hankali.

PDP ta dakatar da yakin neman zabe

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta dakatar yakin neman zabenta na tsawon kwana uku domin adawa da matakin dakatar da Alkalin Alkalan kasar yayin da ya rage makwanni a gudanar da babban zabe.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

PDP ta shaida wa BBC cewa tana son Shugaba Buhari ya janye matakin, yayin da kuma kungiyar lauyoyi ta ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulki.

A na shi martanin, shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki kuma shugaban yakin neman zaben Atiku, ya ce mataki ne da ya sabawa bangaren shari’a da kuma kundin tsarin mulki.

Ya yi gargadin cewa za su dauki mataki idan har shugaban ya ki mutunta tsarin da ya dace wajen cire Alkalin Alkalai.

Batun ko shugaban kasa na da karfin ikon tsige Alkalin Alkalan da ke fuskantar shari’a a kotun da’ar ma’aikata, shi ne ya janyo suka da ce-ce-ku-ce a Najeriya.

A ranar Alhami ne kotun daukaka kara ta umurci kotun da’ar ma’aikata ta dakatar da shari’ar Walter Onnoghen, saboda ba ta da karfin da za ta gurfanar da shi.

Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

An dage shari’ar zuwa ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu, kuma babu tabbas ko kotun da’ar ma’aikatan za ta mutunta umurnin na kotun daukaka kara.

#BBC HAUSA

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: