Amnesty ta gargadi gwamnatin Buhari kan kisan jama’a


0 129

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci sabuwar gwamnatin Buhari ta kawo karshen keta hakkin dan Adam a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty ta ce wa’adin mulkin Buhari na farko an kashe ‘yan Shi’a sama da 350 da kuma masu fafutikar kafa kasar Biafra 150 da aka kashe tsakanin 2015 zuwa 2016.

Kungiyar ta ce tsaro a Najeriya sai kara tabarbarewa ya ke inda ta ce, a Zamfara an kashe daruruwan mutane sannan cikin shekara uku daga 2015 alkalummanta sun nuna kusan mutum 4,000 aka kashe a rikicin makiyaya da manoma.

Kungiyar ta fadi wasu jerin bukatu da suka shafi hakkin bil-Adama wadanda ta ce ya kamata hukumomin Najeriya su mayar da hankali a kai yayin da aka shiga sabon wa’adin mulki a kasar.

Cikin bukatun da kungiyar ta ce idan aka aiwatar da su za su taimaka wajen kyautata hakkin bil-Adama a kasar, sun hada da kare hakkin mata da kananan yara da kuma soke hukuncin kisa.

Hukumomin Najeriya dai sun dade suna yin watsi da rahoton Amnesty, kuma zuwa yanzu babu wani martani da ya fito daga bangaren gwamnatin Najeriya game da sanarwar ta Amnesty.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

A sanarwar dai Amnesty ta ce babban kalubale shi ne yadda ba a hukunta wadanda suka keta hakkin dan adam a kasar.

Mai magana da yawun kungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi, ya shaidawa BBC cewa batutuwan kare hakkin bil’adama da Amnesty take son gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali a kai za su yi tasiri ga zaman lafiya da tattalin arziki.

Ya ce yawan kashe-kashe da ake shi ne ya fi tayar wa Amnesty hankali inda ya ce ya kamata gwamnati ta daraja rayukan ‘yan kasa.

“A wasu kasashe idan aka kashe mutum daya ko biyu, dole sai shugaban kasa ya yi magana.”

“Amma yadda ake kashe-kashe a Najeriya ya nuna daukar ran dan adam bai kai komi ba, za a kashe mutum 100 amma kuma ba za a yi magana ba,” in ji shi.

Kungiyar ta ce sanarwar da ta fitar tunatarwa ce ga alkawari da rantsuwar da gwamnati ta dauka na kare rayuka da hakkin al’ummarta.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.