Wasanni

Nasan Annabi Muhammadu Shine Mutumin da Yafi Kowa a Duniya -Inji Chicharito

Ni ba Musulmi ba ne, Amma Nasan Annabi Muhammadu Shine Mutumin da Yafi Kowa a Duniya Inji Chicharito

Daga Comr Abba Sani Pantami

Duk wadanda suka sanshi sai dai su fadi alheri, nagarta da kuma kyawawan halayyarshi.

Wadanda suka karanta tarihinshi a natse, suna yawan yabawa tare da jinjinawa irin rayuwar da yayi a duniya.

Chicharito dan wasan kwallon kafa ne na kasar Mexico wanda ya bayyana Annabi a matsayin mutum mafi nagarta a duniya, duk da kuwa Kirista ne.

Wadanda Suka sanshi ko suka karanta wani abu a kan shi, sun san irin albarkatacciyar rayuwar da yayi.

An gano cewa ‘yan kwallo da sanannu a duniya na nuna mishi soyayya saboda tarihin shi da suka samu. Wanna ba kowa bane sai Annabi Muhammad SAW.

An turo shi ne zuwa ga mutane baki daya. Ba Annabin musulmai bane kadai, dukkan mutane ne za a musu hisabi da zuwanshi.

Wani babban dan wasan kwallon kafa daga kasar Mexico, Javier Hernandez Balcazar wanda aka fi sani da ‘Chicharito’ ya shiga sahun masoya Annabi.

A daya daga cikin wallafar da yayi a shafinshi na tuwita, ya bayyana irin kaunar da yake wa manzon ta yadda ya ce shi ne mutum mafi nagarta a duk duniya.

Duk da ko Chicharito mabiyin Katolika ne, rayuwar Annabi ta matukar burgeshi har ya bayyana abinda ke ranshi.

Chicahrito ne dan kwallon kafa na farko a kasar Mexico da yayi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Ya halarci wasan gasar kwallon kafa ta duniya a 2010. An karamashi bayan da yaci kwallaye 7.

Abun farin ciki ne da jin dadi idan kaga wadannan mutanen suna karanta tarihin Annabi kuma sun bayyana kaunarsu gareshi. Allah ya kara tabbatar da mu cikin addinin musulunci da shiriya ta gaskiya.

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: