Amina Amal Ta Bukaci Hadiza Gabon Da Ta Biyata Diyyar Miliyan 50, Na Cin Zarafi


2 759

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jarumar Kannywood Amina Amal tam aka abokiyar aikinta Hadiza Gabon a wata Kotun Tarayya da ke Jihar Kano bisa zargin cin zarafin da wulakanta ta.

A takardar sammacin da Aminiya ta gani, Amina Amal ta yi karar Gabon a kotun inda ta bukace ta da biya ta diyyar Naira miliyan 50, sannan kuma ta ba ta hakuri a rubuce, wanda za a wallafa a jaridun kasar nan manya guda biyu.

Idan ba a manta ba, a makon jiya ne Amina Amal ta saki wasu hotuna waxanda suke nuna wasu sassan jikinta, wanda hakan wasu ciki hard a Hadiza Gabon suka yi Allah-wadai da hotunan, wanda hakan ya sa Amina Amal da sake yin wani rubuta, inda ta zargi Hadiza Gabon da madigo.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

- Advertisement -

Daga baya kuma aka ga wani bidiyo, inda aka jiyo muryar Hadiza Gabon tana tambayar Amal tare da dukanta domin ta fadi abin da ke tsakaninsu, wanda daga baya kuma Amina Amal din ta tabbatar da cew kazafi ta yi Gabon din.

Amma kuma kwatsam sai Amal ta kai kara kotu bisa zargin dukan da aka mata, wanda ta ce an ci zarafinta, kuma an tozartata.

Ga takardar sammacin nan a kasa:

 

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.