Amarya Da Ango Sun Mutu Ranar Da Aka Daura Musu Aure

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ma’auratan sun yi hatsarin ne sa’a biyu bayan an daura musu aure

Wata amarya da angonta daga jihar Texas ta Amurka sun mutu sakamakon hatsarin da jirgi mai saukar ungulun da ke dauke da su ya yi lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin liyafar aurensu, in ji wasu jami’ai.

Will Byler da Bailee Ackerman Byler dukkansu dalibai ne a Jami’ar Sam Houston. Wata jaridar dalibai ce ta soma ba da rahoton hatsarin nasu.

Talla

Sun yi hatsarin ne a kusa da Uvalde, kimanin mil 85 da yammacin San Antonio.

Mutanen da suka halarci liyafar tasu sun yi ta mika ta’aziyyarsu a sakonnin da suka wallafa a shafukan zumunta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

“Na yi matukar kaduwa!” In ji wani abokin ango a sakon da ya wallafa a Facebook, yana mai karawa da cewa matukin jirgin ma na cikin wadanda suka mutu.

A wata sanarwa da shugaban daliban jami’ar ya fitar, ya ce za a rika tunawa da ma’auraan saboda kirkinsu.

Ma’auratan sun yi hatsarin ne sa’a biyu bayan an daura musu aure.

Jaridar da ake wallafawa a jami’ar ta ruwaito cewa Will Byler na karantar aikin gona kafin mutuwarsu.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: