Labarai

AL’UMMAR JIHAR KANO SUN JINJINA BAJINTAR A. A. ZAURA A DAIDAI SHIGARSA JAM’IYYAR APC

DAGA Shariff Aminu Ahlan
A ƙasa da sati ɗaya da gudanar da babban biki mai cike da tarihi da ɗaukar ido da ya shirya Kano zuwa zumuɗi inda aka yi masa maraba zuwa cikin jam’iyya mai mulki a hukumance tare da ƙayataccen shagali da ɗumbin taron jama’a da zunzurutun haɗakar magoya bayan jam’iyya da tulin masoya daga loko da saƙo na wannan Jiha wanda abin ƙayatarwa har da membobi daga ɓangaren ƴan adawa waɗanda su ke nuna goyon bayansu a bayyane da yarda da mutumin da ya sauya sheƙar zuwa jam’iyyar gwamnati. Matakin tattaunawar cikin nasara ya tafi gare shi da ɗumbin mabiya da jefa razani.

Wa ne ne mutumin? Ba kowa ba ne face mutum mai manufa, Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura, wanda aka fi sani a A.A Zaura.

Bari na faɗi wannan yanzu, duk wani wanda ya ke da alaƙa da siyasa a Jihar Kano zai kasance da ni wajen shaida cewa babu wani abu irin wannan da aka taɓa shaidawa a tarihin jam’iyyar inda sabon zuwa wanda ya ke kan matakin farfaɗowa da tsohon tsarinsa da samar da haɗakar yarjejeniyar mu’amalar siyasa da sauran manyan gawurtattun ƴan siyasa da ke ɓata hankalin dare kan maganar siyasa dangane da yadda za su samu sauran ƙarin ƙarfi da jiga-jigan siyasa masu tasiri.

Ba shakka, ɗumin zuciya ne da nuni da abun jin daɗi ga ɗumbin mabiya da magoya bayansa waɗanda su ke tafe a kodayaushe domin ba da sanarwa da shaida buɗaɗɗen goyon baya ga mutumin da zuciya ta yi imani da goyo baya mai yawa kan tafiyar siyasrsa da ɗoki na haƙiƙa da shirin ba da kai da sadaukarwa kan goyon bayan burinsa na siyasa kan kowane irin matsayi da zai iya kasancewa.

Tashinsa kan matsayin gadon siyasar Jiha abin mamaki ne a kalla. A matsayin mutum wanda kullum ya ke tashi da ƙulla alaƙa da ƴan siyasa daga sama har ƙasa, wani zai iya dukan ƙirjinsa cikin ƙarfin gwiwa sannan zai iya faɗar hakan anan, haka zalika yanzu ya san cewa mutumin da ake ta magana akai da yawan hasashe wani ne wanda zai iya jan kwale-kwale da shawo kansa idan iskar haƙiƙanin furannin siyasa su ka taso da haɗe dukkan ƙarfi gaba ɗaya.

Mafi yawan tattaunawar da ake mutane da dama su na da shauƙin ya nemi takarar gwamna, wanda ya gwada a jam’iyyar da ya baro a lokacin da aka ƙulla alaƙar siyasa da gwamnati mai ci ya yarda ya janye ya umarci magoya bayansa su zaɓi jam’iyya mai ci duk da kasancewar shi ke riƙe da jam’iyyar komai ya na hannunsa.

Masu nazari da sharhin siyasa sun yi imani cewa haziƙin mutum na musamman Zaura sai sake sabunta daɗaɗɗen ƙudirinsa da burinsa ya jagoranci wannan Jiha. An yi imani kuma zai iya karawa tare da yin nasara akan duk wani ɗan siyasa da zai nemi karawa da shi kan neman wannan takara mafi ƙarfi a Jihar ba batu ne na matakin gogewa da jimawa a cikin jam’iyya da yawan mabiya da ƙulli da kuɗi ko ƙwarewa kan tsarin siyasa ba.

Zaura ya na da wani abu sama da ka iya ba shi nasara babba wacce ba a tsammani kan duk wani abokin adawa da zai tsaya a hanyarsa. A taƙaice, bincike da gwajin membobin jam’iyya cikin ƙarfi an yi imani da ƙirƙirar matasa da burinsu da ƙwarewarsu ta musamman kan wasa wajen iya yanke hukunci mai kyau cikin nutsuwa a siyasa da kan kai shi ga samun tikitin tsaya takarar daga ƙarshe.

Babu mamaki kan yadda ɗumbin ƙungiyoyin siyasa da rukunoni masu ƙarfi su ke da manufa mai ƙarfi ta ƙulla alaƙa da shi da amincewa da shi da jagoranci bisa buri da zumuɗin haɗewa da jirgin nasara kan tafiya mai kykkyawan sakamako a madakata.

Ilimin siyasa, yanayi ne mai riƙiɗa da ɓoyayyen al’amari ga mutanen Jiha ba tare da kaɗan ɗinsu na kokwanto ba za ta iya mamaye kowacce Jiha a tarayya. An albarkance su da kyautar murmushi wanda zai riƙe musu kowane irin wasan siyasa ko da kafin lokacin fara haƙiƙanin yaƙin ne. Ra’ayoyin ba abu ne mai sauƙi a watsar ko su ƙasƙanta ba.

Abubuwa da dama za su iya zama mara baya ga waɗannan juyin-juya-halin muhimman abubuwa. Mutum da ke da ayar tambaya, Zaura, sabon memba ne mai daraja, sai dai tsammaninsa ta bayyana kanta, daɗi da ƙari, sabon memba da tsohon memba a kowacce jam’iyya duk magana ce ta yawan mabiya. A matsayin siyasa na wasa na yawan mabiya a filin daga, Abdulkareem Zaura babu mai galaba a kansa. Ya na da ɗumbin mabiya a tare da shi da kuma wasu da dama da su ke jiran ya karɓe su.

Daɗi da ƙari, ƴan siyasar wannan zamani namu, mafi yawansu su na shiga siyasa ne da manufar neman hanyar azurta kai da zuriyarsu da ba a ma haifa ba, ba tare da la’akari da ɗumbin talakawan da su ka hau layi su ka zaɓe su ba sannan su karɓi dukiya da sunansu da tabbatar da ba su kykkyawar rayuwa, amma a madadin hakan sai su cinye komai.

Sai dai aikinmu na kai da kai ne, sannan cikin ƙarfi aka samar da kuɗaɗe tare da kasuwanci da masana’antu a duk duniya. Dukiyarsa ta samu ne sanadiyyar aiki tuƙuru da juriya da ɗaukan hanyar kasuwanci mai kyau.

Ba ɗan siyasa ba ne mai neman tara dukiya da satar kuɗi cikin sauƙi ba, manufarsa shi ne samun mulki domin kyautata rayuwar al’umma da inganta tsayuwarsu tare da gadar musu da abin tarihi wanda za a riƙa tunawa ba tare da an manta ba har abada. Mutum ne da ya yarda ya dasa bishiya ta tsiro domin a amfana.

Mutane da yawa sun yi imani Alhaji Zaura zai yi duk abin da ake buƙata babu kokwanto cikin ƙarfin gwiwa da tattala dukiyar al’umma domin cigaban Jiha gaba ɗaya. Abubuwan alkhairi na jinƙai da ya yi su na nan da yawa a bayyane. Kamar gwamna na yanzu, Dakta Ganduje wanda duniya ta yi duba da yabawa kan ɗumbin ayyukan cigaba da ya aiwatar a duk faɗin Jihar. Babu shakka A.A Zaura zai zama nagartaccen magaji wanda za a yi alfahari.

Mafarki ne da fata na gwamna Ganduje kamar kowane shugaba mai nasara ya ga ya gadarwa Jiha shugaban da zai ɗora kan cigaba da gudanar da ayyukan cigaba a kowane fanni.

Duk wanda ya ke sauraren shirye-shiryen siyasa da dama zai ji maganganunmu a kullum ta hanyar kafafen sadarwa masu zaman kansu daban-daban wajen sanin haƙiƙanin ayyukan jin ƙai da mutumin ya ke aiwatarwa ga al’ummar Jihar ba tare da nuna bambancin jam’iyya ko siyasa ba.

Duniya za ta faɗi yadda mutumin ya ke jiɓintar lamarin ƴaƴan talakawa daga dukiyarsa ta ƙashin kansa domin su samu nasarar zana jarrabawa cikin nasara, dubban mutane sun amfana daga wannan taimako. Baya da haka, bayanai sun adana yadda mutumin ya ke ba da tallafin kuɗi Naira dubu ashirin ga duk wata mace mai juna biyu da aka kwantar a asibiti wacce ta ke cikin halin neman taimakon kuɗi ta ƙarƙashin haɗaɗɗiyar gidauniyarsa ta A.A Zaura Foundation.

Haka zalika, ba abin mamaki ba ne ga kowa wanda ya shaida irin wannan aikin alkhairi da ɗumbin mabiyan siyasar Malam Zaura ba, wanda tsawon lokaci ya na yin abubuwan alkhairai babu tsammani masu girma da yawa har sun zame masa ma jiki.

Duk da cewar a haƙiƙanin gaskiya bai fito fili ya bayyana ƙudirinsi ko muradinsa ga jama’a ba, amma manyan takalma da ƙanana da ƴan jam’iyyu sun gabatar da ƙididdigarsu sun kuma yi ittifaƙin ya na shirin shiga fafatawar neman takarar gwamna a jam’iyyar.

Tabbas abin mamaki ne kallon yadda fafatawar neman takarar gwamna za ta kasance a 2023, kowa zai buga kalar wasansa yadda ya ke so da abubuwan barkwanci da mamaki da bandariya da wasa daban-daban. Koma dai yaya ne, Zaura zai kasance Zaki da zai shirya yin gurnani.

Waɗanda su ke da kusanci da shi ko su ka samu tattaunawa ko zama da shi, su kan gane cewa mafi yawan ambato da magana game da ƴan siyasa a Kano kamar mutumin ne zuwa ƙofa ta gaba. Mai ƙanƙan da kai da karamci da sauƙin hali da mutunta kai.

Da yawa wataƙila za su ja da baya idan za su bayyana yadda sunansa ya ke yaɗuwa kamar wutar daji, mutumin bai bayyana maganar awa tun bayan komawarsa jam’iyyar gwamnati ba.

Duk da shirunsa da lissafinsa kan yanayin siyasar Jihar, mutumin a kullum ya na sanya murmushi a fuskokin ɗumbin jama’a magoya bayan gwamnatin a mataki daban-daban waɗanda aka sani da waɗanda ba a sani ba. Amma zahirin gaskiya shi ne kowa ya san cewa Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura tabbas ya shirya bugun gida zuwa ga sabon tsari.

Ahlan Malami ne a kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, ya rubuta daga Jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: