-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Allah Ya Yi Wa Khalifa Isyaka Rabi’u rasuwa


0 708

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Allah ya yi wa Shugaban Darikar Tijjaniya a Najeriya Kahlifa Isyaka Rabi’u, rasuwsa, kamar yadda daya daga cikin ‘ya’yansa ya shaida wa BBC.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ya shaida wa BBC cewa ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan na Ingila a yammacin ranar Talata.

Marigayin, wanda ya sha fama da rashin lafiya a ‘yan kwanakin nan, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya.

Baya ga malantaka, marigayin kuma hamshakin dan kasuwa ne wanda ya yi fice a fagen kasuwanci a Najeriya.

Bayanai sun za a yi janazar marigayin da zarar gawarsa ta iso Najeriya daga birnin Landan, inda ya rasu.

Ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 42 da kuma jikoki da dama cikinsu har da Alhaji Abdussamad Isyaka Rab’iu, wanda shi ne shugaban hadakar kamfanin BUA.

Grey line

Tarihin Kahlifa Isyaka Rabi’u

 • Bayanai sun nuna cewa an haifi marigayin ne a 1928
 • Ya yi karatun AlKur’ani da na adidni a birnin Kano
 • Kafin daga bisani a tura shi birnin Maiduguri na jihar Borno domin kara karatu
 • Ya koma Kano inda ya ci gaba da koyar da karatun Kur’ani da na addini
 • Daga baya ne kuma ya fara harkokin kasuwanci inda ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons
 • Ya yi fifce matuka a fagen kasuwanci da na karatun Alkur’ani
 • Daga bisa ni an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya
 • Harkokin kasuwancin da ‘ya’yansa suka gada kuma suka ci gaba da samun daukaka a kai

Ayyukan jin kai

Darikar Tijjaniyya na da magoya baya da dama a Najeriya
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku’ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da “Khadimul Kur’an”.

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

Sai dai har ya rasu ana ja-in-ja tsakanin jama’arsa da na Sheikh Dahiru Usman Bauchi kan wane ne ya fi cancantar wannan mukami.

Ya kuma yi suna wurin tallafawa marayu da marasa galihu.

Marigayin, wanda amini ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, da Alhaji Aminu Dantata, yana daga cikin fitattun dattawan da suka rage a jihar.

Grey line

Bayani kan darikar Tijjaniya

 • An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784
 • Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta
 • Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin Afirka
 • Tana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya
 • Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girma
 • Sun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:
 • Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita Allah
 • Sai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta wa
 • Ana alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta dama
 • An haife shi a kasar Senegal kuma jama’a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsa
 • Darikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Najeriya inda suke da mabiya sosai

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.