Alkali Ya Kashe Masa Aure Na Biyu Da Yayi

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wata Kotu a jahar Bauchi ta warware igiyar wani aure na biyu bayan da aka tabbatar da cewa mijin ya kara aure na biyun ne da keke Nape din da matarsa ta saya masa bayan ta sayar da gonar gado ta saya masa keken tunda bai da aikin yi don a rufawa kai asiri.

Daga bisani ya sayar da Keke Nape din ya kama haya kuma ya rangada sabon aure na biyu.

Mijin matar mai yara biyar an tabbatar da cewa yaransa uku a gidanjen abokansu suke kwana saboda gidan da suke ciki babu inda yaran za su rinka kwana.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 782

Sai dai mijin ya kada baki inda ya ce, aure nufi ne na Ubangiji kuma Allah ne yake ciyar da bawa ba wayau ko darbarasa ba inda ya ce yana da kwarin baya da ya ke ganin mace daya ba za ta gamsar da shi ba.

A ra’ayinku, kuna ganin alkali ya yi masa adalci da ya kashe masa auren sabuwar amaryarsa?

©Zuma Times Hausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: