-Fitaccen jarumin finafinan Hausa ya zama jakadan hukumar kula da sadarwa ta kasa NCC a yayin makon bikin amfani da wayar sadarawa
Jakadancin Ali Nuhu a hukumar ya hada da sa hotunansa a dukkanin tallace-tallece na hukumar manyan alluna da jaridu da mujallu da kuma sauran takardu sanarwa.
-Shirye-shirye sun kammala don kaddamar da gangamin masu amfani da wayar sadarwa a Najeriya a ranar Laraba 15 ga watan Maris na shekarar 2017.
Hukumar sadarwa ta kasa NCC ta zabi jarumin finafinan Hausa Ali Nuhu a matsayin jakadanta a shirye-shiryen ta ke yi na gudanar na bikin kaddamar da gangamin makon masu amfani da wayoyin sadarwa.
A wata sanarwa da Mista Tony Ojobo kakakin hukumar ya sa hannu ta ce, za a gudanar bikin kaddamar da gangamin ne a ranar Laraba 15 ga watan Maris, wanda ya zo dai dai da ranar kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta duniya mai taken “samar da na`urorin da mai amfani zai aminta”
Babban batu a taron da za a gudanar a shalkwatar hukumar NCC a Abuja shi ne, fito da dabi’un masu amfani da tarho a Najeriya.
An zabi wasu manyan masu nishadantarwa guda 2 ciki har da Ali Nuhu don su nuna yadda dabi’ar mai amfani da kayayyaki ta ke. A cewar sanarwa.

Ali Nuhu da wasu manyan jami’an hukumar NCC
Mai masaukin baki a bikin, kuma shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar G. Dambatta, a wani jawabi da yayi a lokacin ba Ali Nuhu jakadancin ya ce, kare hakkin masu amfani da tarho da samar da ‘yanci, su ne ginshikan manufofin shugabancinsa guda 8.
Kuma saboda haka ne hukumar ta sadaukar shekarar 2017 ga jin dadin masu amfani da wayar tarho wadanda suka hada da muhimman batutuwa a shekarar ta jin dadin masu amfani da wayar tarho wadanda suka hada da;
Wayar da kai game ingancin aiki, dandalin lantarki da mayen karfe (EMF), da Kar a dame ni (DND) wanda za a yi amfani da shi wajen tsayar da sakwannin ba gaira ba dalili da kuma kira kyauta zuwa hukumar a yayin da kamfanonin layin wayar salula su ka kasa yin wani abu game korafin jama’a.
Kamfe din na fatan samun goyon bayan masu kamfanonin wayar salula do cimma manufar samun ingancin aiki musamman katsewar kira.
Kwanannan hukumar ta samu labarin zanga-zangar rashin inganci musamman katsewar kira da rashin karfin sabis.
Shekarar ta kamfe din masu amfani da wayar salula za kuma ta gabatar da wani shiri mai taken “NCC Consumer Conservation” wanda hukumar ta shirya a duk yankunan kasar nan guda shida.
Ali Nuhu na daya da cikin fitattun jaruman finafinan Hausa da ke jan hankalin matasa a da kuma sauran jama’a da irin salonsu na nishadantawa.
Jakadancin Ali Nuhu a hukumar ya hada da sa hotunansa a dukkanin tallace-tallece na hukumar manyan alluna da jaridu da mujallu da kuma sauran takardu sanarwa.
Souce Code In 24wikis.com
Add Comment