Iyalan marigayi Tijjani Ibrahim sun karbi kyautar da aka ba mahaifinsu a bikin kannywood Awards.
A wani hoto da babban dan marigayin Saleem Tijjani Ibrahim ya sa a shafinsa na sada zumunta da muhawara na Facebook, ya nuna Ali Nuhu na mika kambin da aka ba marigayin a yayin bikin kannywood Awards da aka yi a Abuja ga Saleem din.
A baya, babban dan marigayin ya nuna rashin jin dadinsa na rashin gayyatarsu bikin da ya ce ba a yi ba, su kuma masu gudanar da bikin na cewa sun aika da gayyata ba su san cewa sako bai je ba.
Marigayi Tijjani Ibrahim na daya daga cikin shahararrun masu ba da umarni a fina-finan Hausa, kuma cikin na farko da suka samu horo a Amurka a aikin talbijin a shekarun 1980.
Add Comment