Akwai Sojojin Da Ba Musulmai Ba Da Suke Yi Wa Fulani Makiyaya Kisan Zalunci Saboda Bambancin Addini, Cewar Sheik Ahmad Gumi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Datti Assalafiy

Sheikh Dr Ahmad Gumi (H) ya mayar da zazzafan raddi cikin harcen turanci ga babbar kungiyar mabiya addinin nasara a Nigeria saboda suna kokarin hadashi rikici da Gwamnatin tarayya.

Malam ya tunatar da su cewa har yanzu yana kan matsayarsa na cewa akwai sojoji wadanda ba Musulmi ba wanda suke kisan zalunci wa fulani makiyaya saboda banbancin addini.

Malam yace tun a farkon jamhuriya ake wannan zalunci na kisan Musulmi, ya tunatar da kungiyar mabiya addinin nasaran irin kisan banbancin addini da aka yiwa Musulmai ‘yan mazan jiya su Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, wanda ‘ya’yanta irinsu Nzoegwu, Dimka da Gideon Orkar da sauransu suka aiwatar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 732

Sannan Malam yace farkon wadanda suka fara jagorantar aiwatar da kisan kiyashi na banbancin addini kan fulanin jeji makiyaya a dajin Birnin Gwari Kaduna a shekarar 2014 ba Musulmi bane, sunansu General Malu da Colonel Folawole karkashin jagoranci da umarnin shugaban sojojin kasa na wancan lokacin Lieutenant General Minimah da Major General Kenneth C. Osiji lokacin yana GOC rundina ta 1 a nan Jihar Kaduna.

Malam ya ce idan wannan kungiya ta masu bin addinin Nasara tana da ja akan abinda ya fada cewa ‘ya’yanta sojoji suna kashe fulani makiyaya saboda banbancin addini su kaishi kotu yazo ya kare kansa mana, amma menene yasa suke kokarin hadashi rigima da Gwamnatin tarayya da kuma sojoji?

Raddi ne wanda ya cancani a rubuta shi da tawadar danyen zinare.

Yaa Allah Ka tsare mana Sheikh Dr Ahmad Gumi daga makircin bakaken yahudawa, Allah Ka ba shi nasara a kansu.
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: