– Hukumar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ce mutane 11 suka nutse a koguna
– Hukumar ta ce mutanen sun hada da yara da manya a watan da ta gabata
– Kakakin hukumar ya ce duk wanda bai iya yin iyo ba su daina yin wanka ko kamu kifi a kandami ko kogi
Hukumar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ce akalla mutane 11 suka nutse a wasu koguna a jihar a tsakanin wata daya da ta gabata.
Sanarwar da mai magana da yawun hukumar, SP Abdu Jinjiri ya bayar a Dutse a yau Talata, 8 ga watan Agusta yayin da ya bayyana yawan mutanen da suka nutsar a cikin wannan lokacin.
Hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa ta nuna damuwa mai tsanani game da yawan mutanen da suka nutsar a jihar, wannan mummunar al’amari ya faru ne a wurare irin su Ringim, Guri, Kiyawa da kuma Dutse, wadanda suka hada da yara da manya a watan da ta gabata.
Kamar yadda Arewablog.com ke da labari, Jinjiri ya shawarci jama’ar yankin cewa duk wanda bai iya yin iyo ba su daina yin wanka ko kamu kifi a kandami ko kogi.
Jinjiri ya kuma bukaci iyaye da masu kula da su saka idanu ga ‘ya’yansu don rage wannan al’amarin.
Source Naij Hausa
Add Comment