Labarai

Aisha Buhari Za Ta Sauki Matayen Shugabannin Kasar Afirka Ta Yamma

Uwar gidar shugaban kasar Nijeriya, Hajiya Aisha Buhari za ta sauki matayen shugabannin kasashen Afirka ta yamma a ranar 28 ga wata Fabrairu, 2017
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban darakatan yada labarai na ofishin matar shugaban kasa, Suleiman Haruna ya fitar a jiya Litinin
Haruna ya ce, taron zai mayar da hankali ne kan tattauna batun yadda za a inganata rayuwar mata ‘yan gudun hijira da kuma kananan yara a yankin kogin Chadi.
Daga cikin uwayen gidan shugabannin kasar da ake sa ran za su halarci taron sun hada da: Matar shugaban kasar Nijar, da ta Kamaru, da ta Chadi, da ta Benin, da ta Burkina Faso, da ta Mali da kuma kungiyoyin fararen hula
Taron zai mayar da hankali kan yadda za a tsara yadda za a ke kula da ‘yan gudun hijira da kuma yadda za a ke samar musu da abubuwan more rayuwa da kuma yadda za a taimakawa mata da yara wajen koyon sana’o’i da kuma ilimi.