Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta tallafawa wasu Marayu 60 da guraben karo ilimi a garin Daura da ke jihar Katsina.
Uwargidan Shugaban ta bayyana tallafin a matsayin gudunmawarta ga al’umma inda ta nuna cewa ilimi ne kadai za ka yaro, ka taimaka masa a rayuwa.
A bisa Tallafin, Aisha Buhari za ta dauki nauyin karatun matakin ilimin Firamare na marayun har su kammala.
Add Comment