Aisha Buhari Ta Shiryawa Shugaba Buhari Tawagar Yakin Neman Zabe Duk Da..

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A’isha Buhari ta shiryawa shugaba Buhari tawagar yakin neman zabe duk da a baya tayi barazanar kin goyon bayanshi

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari da alama ta yi amai ta lashe akan goyon bayan mijinta a sake neman kujerar shugaban kasa a karo na biyu,

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

APC Knows It Will Loose Woefully In 2023, PDP Chieftain…

1 of 86

A baya dai A’isha Buhari a wata hira da ta yi da BBC hausa a shekarar 2016 ta bayyana cewa idan mijin nata baiyi canje-canje ba a wasu bangarorin gwamnatinshi ba ba lallai ne ta sake fitowa ta taya shi yakin neman zabe ba.

A yanzu dai Aisha Buhari ta shiryawa mijin nata tawagar yakin neman zabe me dauke da membobi 700 ciki hadda ita kanta wadda itace zata shugabanci tawagar sai kuma matar mataimakin shugaban kasa da ministoci da matan gwamnoni da sanatoci da tsaffin gwamnoni da manyan ma’ikatan gwamnati da masu nishadantarwa dadai sauransu.

A ranar Alhamis me zuwa ake sa ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kanshi zai kaddamar da wannan tawaga, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: