Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta dawo Najeriya a jiya inda ta halarci wani taro a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Daraktan bayanai na uwargidan shugaban kasa, Suleiman Haruna, ya bayyana cewa Aisha Buhari ta fara sauka a Abuja, inda daga nan ta dauki hanyar Owerri, inda ta yi matsayin uwar taro na taron Agusta 2017 wanda akayi ma lakabi da “Building Bridges of Friendship across the Niger” wato dinke barakar abota a fadin kasar Najeriya.
Gwamna Rochas Okorocha tare da matarsa, wadanda suka shirya taron “shekara-shekara na Agusta” ne suka tarbi uwargidan shugaban kasar a filin jirgin sama na Sam Mbakwe Cargo International Airport dake Owerri.
Da take magana a wajen taron, Aisha Buhari tace: “Wannan taro na bikin mata ne.yana da matukar muhimmanci saboda a irin wannan taro, mata ‘yan kabilar Igbo na tattaunawa kan al’amura na ci gaba da kuma wanzuwar zaman lafiya a ko wani mataki.”
Uwargidan Buhari ta bayyana cewa iyaye mata na da mahimmiyar rawa da zasu taka wajen kawo hadin kan kasa duk kuwa da banbance-banbancen siyasa, addinai da kuma al’ada.
Ta ba mata tabbacin cewa zasu samu goyon bayanta a duk lokacin da suka shirya dukkan taro da zai kawo cigaban su.
Source Naij Hausa
Add Comment