Aikin Gada Mafi Tsayi Da Shugaba Buhari Yakeyi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Wasu jami’an gwamnatin Shugaba Buhari sun kai ziyarar gani da ido wa aiki gada mafi tsawo a Arewacin Nigeria, itace gadar data tashi daga Loko cikin jihar Nasarawa zuwa Oweto cikin jihar Benue, tana da nisan kilometer 2.2 (Biyu da digo biyu), za’a kammala ta cikin wannan shekara da yardan Allah, Shugaba Buhari ya fitar da kudi sama da Naira biliyan 8 domin aikin.

Itace gada mafi tsayi a Arewacin kasar nan, kuma idan an kammala ta zata kasance hanya mafi sauki kuma mafi kusa da zata hada Arewacin Nigeria da da jihohin Inyamurai, an shafe sama da Shekaru 50 ana fatan ayi wannan gadar wacce take kan ruwa mafi yawan ta, amma ba’a samu wata gwamnatin data yi haka ba, sai ta farar hula na Shugaba Muhammadu Buhari, wani kamfanin kasar China ne yake aikin tare da kamfanonin Nigeria guda 9, kuma za’a kare a shekarar nan ta 2019, idan Allah ya amince.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

#Abdulhadi Isah

Talla
Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: