Ahmed Musa Ya Gwangwaje Wata Mace Da Danta Da Kyautar N250,000


0 398

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ahmed Musa, a Dan zaman da ya yi sansanin atisaye a garin Asaba ta jihar Delta, tsakanin 22 zuwa 26 ga watan Maris, don wakiltar Nijeriya a wasannin share fagen cin kofin Afirka, ya faranta zuciyar wata baiwar Alllah da ta zo neman aikin share- share na tsawon kwanakin da ‘yan wasan za su yi a sansanin.

Matar dai ta zo ne da danta domin neman aikin N3,000, amma sai Ahmed Musa ya ja ta gefe ita da danta ya yi wata tattaunawa da ita na ‘yan mintuna.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

A tattaunawar ne Ahmed Musa ya karbi lambar asusun bankin matar, inda nan take aka ji matar ta kwala ihu tana shi wa Ahmed Musa albarka.

Ashe ko da karbar akawunt numbarta, bai yi wata-wata ba sai ya yi mata taransifar N250,000.

An ci gaba da yabawa dan wasan bisa wannan taimako da ya yi. Da fatan Allah ya saka masa da alkhairi, amin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.