Sports

Ahmad Musa Ya Gwangwaje Wasu Yaransa Ukku Na Tun Asali Da Maka Maka Gidaje Gidaje Kyauta A Jihar Kanò

ABIN ALKHAIRI: Captain Ahmad Musa Ya Gwangwaje Wasu Yaransa Ukku Na Tun Asali Da Maka Maka Gidaje Gidaje Kyauta A Jihar Kanò

 

Fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya Captain Ahmed Musa MON ya gwangwaje wasu yaransa na tun asali da kyautar gidaje na alfarma a birnin a birnin Kano.

 

Yaran sun kasance tare da Ahmad Musa tun zamanin da can kafin ya samu ɗaukaka da cigaban rayuwa. Wannan ta sa Ahmad Musa ya tuna baya ya waiwaice su a yanzu ya saya musu gidaje kyauta su zauna da iyalansu.

 

Mutanan da ya sayawa gidajen sun haɗa da::

Adamawa Sulaiman. Auwal Umar Black . Hamisu BabaLe da kuma Abbati Shehu.

 

Ahmad Musa mutum ne mai juriya wanda ya ke ƙoƙari da himma wajen kyautata rayuwar al’umma. Gabaɗaya rayuwarsu ya na tafiyar da ita ne akan taimako da jinƙan masu rauni da marasa ƙarfi.

 

Wannan wata ƴar manuniya ce da ke ƙara fito da nagartarsa a fili cewa Ahmad Musa mutum ne wanda ba ya mance baya, ya na ƙoƙari wajen kyautatawa mutanen da su ka taso tare tun kafin ya zama wani bayan ya zama wanin bai manta su na.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.