Labarai

Afirka Ta Kudu: Shirin Sahale Wa Mata Auren Miji Fiye Da Daya Ya Janyo Ce-ce-ku-ce

Afirka Ta Kudu: Shirin Sahale Wa Mata Auren Miji Fiye Da daya Ya Janyo Ce-ce-ku-ce

Wani shiri da gwamnatin Afrika ta Kudu ta fito da shi na ba mace damar auren namiji fiye da daya ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Sai dai hakan bai zowa da Farfesa Collins Machoko da mamaki ba, wanda kwararren malami ne a wannan fanni.
Ya shaida wa BBC cewa al’ummar Afrika ba su shirya wa daidaito ba. ”Ba mu san yadda za mu rika tafiyar da mata ba.” in ji shi.

Afrika ta Kudu na daga cikin kasashe duniya da ke amfani da kundin tsarin mulki da ya ba al’umma damar zabar abin da ransu ya ke so.

Misali tana daga cikin kasashen da suka yadda da auren jinsi da kuma auren mace fiye da daya ga mazaje.

Musa Mseleku, dan kasuwa ne da ke auren mata hudu, kuma bai yadda da mace ta auri namiji fiye da daya ba.

A cewarsa ”hakan zai rusa al’adar Afrika. Ya matsayin ‘ya’yan da aka haifa zai zama? Ta yaya za su san asalinsu?”
”Wato ana so a ce mace ta zama matsayin miji kenan za ta mallaki maza biyu. To kenan macen ce za ta biya sadakin mazajen da za ta aura?”
”Sannan mazan za su rika amfani da sunanta tun da ita ta ke aurensu?” kamar yadda Musa ya tambaya.

Auren sirri
A binciken da Farfesa Machoko ya yi a kasarsa ta haihuwa wato Zimbabwe mai makwabtaka kan auren namiji fiye da daya ya jiyo ra’ayin duka bangarorin biyu.
Malamin ya tattauna da mata 20 da maza 40 da kowace mace daga 20 din ta auri guda biyu, inda suka bayyana masa cewa suna gudanar da zamansu cikin sirri la’akari da cewa al’ada ba ta yadda da shi ba.

A cewar Mista Machoko ”masu auren namiji fiye da daya na yin komai ne a cikin sirri saboda tsoron al’ummar da suke zaune da su, kamar dai wadanda ke aikata miyagun ayyuka na kungiyoyin asiri.”
”Kuma ma idan har wani ya tunkare su da maganar wanda ba su yadda da shi ba su kan karyata cewa sun aikata hakan saboda tsoron za a tsangwame su cikin al’umma.

Ma’auratan da Farfesa Machoko ya tattauna da su ba zaune suke wuri daya ba, amma sun yadda da auren kuma sun fahimci junansu.

”Akwai daga cikin matan da ta shaida min cewa ta fara sha’awar namiji fiye da daya ne tun tana da shekaru 12, bayan da ta fahimci cewa sarauniyar kudan zuma tana auren maza da yawa, kuma abin na birge ta.

Bayan da ta balaga sai ta fara saduwa tare da duka samarinta kuma duka sun san juna.

”Hudu daga cikin mazaje tara da ta ke aure na daga cikin samarinta na farko,”in ji Mr Machoko.

A tsarin auren namiji fiye da daya mata ne ke nuna sha’awar kulla auratayya ta hanyar neman mazajen don a daura musu aure.

Idan mazan sun so za su iya biyan kudin auren, ko kuma su taimaka wa zamantakewar amma bai zama dole ba.
Kuma mace na da damar sakin daya daga cikin mazajen idan har ta fahimci cewa zai kawo wa zaman cikas.

Farfesa Machoko ya ce daga hirar da ya yi da wasu mazajen sun fada masa cewa kaunar da su ke yi wa macen ya sa suka aminta ta yi musu kishiya, saboda ba su shirya su rasa ta ba gaba daya.

Wasu mazan kuma sun bayyana cewa sun fahimci cewa kwata-kwata ba sa gamsar da matan na su wurin kwanciya, akan haka suka aminta da a yi musu kishiya a maimakon su rabu da matan.
Wasu kuma mazajen ba su da kwan haihuwa wanda hakan ya ke sa su aminta cewa matar ta kara auren wani namiji su zauna tare.

Kuma idan ta haihu za su rika karyar cewa dansu ne don gudun a tsangwame su cewa ba su haihuwa.

A cewar Farfesa Machoko ba ya da masaniyar cewa auren namiji fiye da daya na gudana a Afrika ta Kudu.
Amma a yanzu mai fafutukar ya bukaci gwamnati ta halasta irin wannan aure saboda ba wa mata irin hakkin da doka ta ba maza a kansu na auren mace fiye da daya.

Bukatar hakan na cikin kundin da hukumomi suka kira ‘Green Paper’, wadda gwamnati ta fitar na bukatar yin garambawul ga dokokin aure a karon farko tun bayan shekarar 1994.

A cewar Charlene May wata mai fafutuka daga wata kungiyar lauyoyi mata a Afrika ta Kudu ba za su sa ido a tauye hakkin mata ta ko wace hanya ba.

A cewarta ”ba za mu yi watsi da sauyin doka don kawai ya kalubalanci ra’ayoyin fifita maza a cikin al’umma ba.”
Sauyin dokar ya kuma shirya ba da ‘yanci ga auratayyar Musulmi da Hindu da Yahudawa da kuma Rastafariya ba.
Sai dai duk da wani bangare na al’umma ya aminta cewa mace ta auri namiji fiye da daya, batun saka shi cikin doka ya samu rashin amincewar malamai da ke cikin majalisa.

A cewar Shugaban jam’iyyar adawa ta Christian Democratic Pary Reberand Kenneth Meshoe, ”Yin hakan zai ruguza al’umma”.

Ya kara da cewa ”za a kai lokacin da daya daga cikin mazajen zai zargi matar da cewa ta fi bai wa kishiyarsa lokaci, kuma hakan zai haifar da rikici tsakanin mazajen.”
A na shi bangaren dan jam’iyyar Musulmi ta Islamic Al-Jamah Party Ganief Hendricks cewa ya yi ” ku yi la’akari da idan an haifi yaro a irin wannan aure dole ne sai an yi gwajin kwayoyin halitta don gano mahaifinsa.”
Har wayau wasu masu adawa da shirin sun bayyana cewa ba kawai don kundin tsarin mulki na son daidaito ba zai aminta da wani abu da zai gurbata al’umma ba.

Amma Farfesa Machoko ya ce an taba gudanar da irin wannan aure a Kenya da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Nijeriya, sannan yanzu haka mata na auren maza da dama a Gabon kuma doka ta aminta da haka.

”Zuwan addinin Kirista da kuma mulkin mallaka ne ya sa matsayin da mata su ke da shi ya dusashe. Ya zama cewa ba matsayi daya su ke da maza ba. Kuma an yi amfani da aure wurin nuna musu bambanci,” in ji Farfesa Machoko.

Ya kara da cewa ”batun mallakar ‘ya’yan da a ka haifa a irin wannan aure mai sauki ne. Maganar ita ce za su zama mallakar duka wadanda auren ya shafa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: