Addini

[Addini] Muhimmancin Samun Jam,in Sallar Asuba

Muhimmancin Samun Jam’in Sallar Asuba
SALLAR ASUBAHI sallah ce mai muhimmanci. Allah ya rantse da lokacinta a cikin al-kur’ani.
Allaah yace:-
( ﻭﺍﻟﻔﺠﺮ ﻭﻟﻴﺎﻝ ﻋﺸﺮ )
Saboda muhimmancin ta ne Allaah ya kirata da sunan “QUR’AANUL FAJR”
Allaah yace:-
( ﺃﻗﻢ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻟﺪﻟﻮﻙ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﺇﻟﻰ ﻏﺴﻖ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﻗﺮﺁﻥ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺇﻥ ﻗﺮﺁﻥ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻛﺎﻥ ﻣﺸﻬﻮﺩﺍً )
Dan uwa za ka tauye wa kanka lada mai yawa idan baka tashi ka je ka sallace ta ba.
Za ka rasa darajoji masu dimbin yawa idan ka gagara tashi don sallarta.
Ka tuna fa ita ce Sallar da take yi wa munafukai nauyi
Manzon Allah (SAW) ya ce Nafilar asubahi ta fi duniya da abinda yake cikin ta.
(( ﺭﻛﻌﺘﺎ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﻣﺎ ﻓﻴﻬﺎ ))
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛـــــــــــــ  ـــــــــﺒﺮ
Idan har raka’atal Fajri ta fi duniya da abinda yake cikin ta, to ya kake ganin ita kanta Sallar Asubahin?
KANA SON A DASA MAKA BISHIYA A ALJANNA?
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya ce ‘Subhanallah, Walhamdulillah, Wala’ilaha Illallah, Wallahu Akbar’, za’a dasa masa bishiya a Aljanna da kowanne daya daga cikin su”.
Silsilatul Ahaadiisus Sahiha 2880.
Me kake tsammani bayan ka idar da Sallah ka zauna ka yi ta wadannan zikirorin?
Me kake zaton ma’anar za’a dasa maka bishiya a Aljanna? Idan bishiyar taka ce Aljannar da bishiyar ke ciki fa? Tabbas taka ce.
Ya Rabbana duk wanda ya tura wannan har wasu suka karanta suka amfana, Ya Allah Ka dasa masa bishiyoyi a Aljanna iya adadin mutanen da suka karanta suka amfana a dalilinsa.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.